Isa ga babban shafi
Mozambique-Ta'addanci

Ta'addanci: Mutane dubu 670 ke gudun hijira a Mozambique

Majalisar Dinkin Duniya tace ‘yan gudun hijira sama da 5 da suka gudu domin tsira da rayukan su daga rikicin da ake yi a garin Palma na kasar Mozambique yanzu haka sun samu mafaka.

Hoton wani yankin garin Palma da ya fuskanci hare-haren 'yan ta'adda a kasar Mozambique.
Hoton wani yankin garin Palma da ya fuskanci hare-haren 'yan ta'adda a kasar Mozambique. AP - Planet Labs Inc.
Talla

Mai Magana da yawun hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Sandra Black, ta ce ya zuwa ranar talatar da ta gabata, sun kidaya mutane dubu 5 da 360 da suka isa yankunan Nangade da Mueda da Montepuez da kuma Pemba.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun mutu sakamakon hare haren ‘yan tawayen masu ikrarin jihadi.

Rikicin ‘yan bindigar yayi sanadiyar raba mutane kusan 670,000 daga muhallansu a yankin dake da arzikin iskar gas.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.