Isa ga babban shafi

Yara dubu 250 na fuskantar barazanar cutuka a Mozambique

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kimanin kananan yara dubu 250 da suka rasa muhallansu sakamakon rikicin mayakan jihadi a lardin Cabo Delgado na kasar Mozambique, na fuskantar barazanar kamuwa da cutuka a daidai lokacin da damuna ke karatowa.

Kananan yara na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalara a Mozambique.
Kananan yara na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalara a Mozambique. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Kimanin mutane dubu 2 da 400 akasarinsu fararen hula, suka rasa rayukansu tun daga watan Oktoban shekarar 2017 sakamakon hare-haren mayakan da ke ikirarin jihadi a lardin Cabo Delgado mai arzikin iskar gas.

Gwamnatin Mozambique ta ce, jumullar mutane dubu 570 suka rasa muhallansu a sanadiyar hare-haren.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce, kananan yara da iyalai sun fuskanci mummunar guguwa da ambaliyar ruwa da fari da matsalar tattalin arziki saboda annobar Covid-19 da kuma rikice-rikice a lardin na Cabo Delgado.

UNICEF ta kuma yi gargadin yiwuwar barkewar cutar kwalara wadda za a iya magance ta ko kuma dakatar da ita, amma duk da haka tana kashe kananan yara muddin aka yi sakacin basu kulawa.

Yanzu haka UNIECF na neman Dala miliyan 52.8 domin gudanar da ayyukan jin-kai a Mozambique nan da shekara mai zuwa, inda za a ware wa lardin Cabo Delgado Dala miliyan 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.