Ivory Coast: An saki gwamman mutanen da aka kama kan rikicin zaben 2020
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya sanar da sakin mutane da dama da aka kama yayin rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar bara.
Wallafawa ranar:
Kimanin mutane 100 suka mutu a rikicin siyasar mai nasaba da zaben da ya gudana a watan Oktoban da ya gabata, wanda shugaba Ouattara ya lashe a wa’adi na 3.
'Yan takara daga bangaren ‘yan adawa sun kauracewa zaben a waccan lokaci, bisa hujjar takaita wa’adin shugabancin kasar zuwa guda 2 da kundin tsarin mulkin kasar ta Ivory Coast yayi.
Jagororin ‘yan adawa da suka hada da Laurent Gbagbo da Henri Konan Bedie dukkansu tsaffin shugabannin kasar ne dai suka sakin fursunonin siyasar.
Gbagbo ya nemi sakin karin mutane fiye da 100, ciki har da wasu da ke da hannu a wani tashin hankalin zaben shekarun 2010 zuwa 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu