Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Alassane Ouattara ya lashe zaben Ivory Coast da gagarumin rinjaye

Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast ya yi nasarar lashe zaben kasar da gagarumin rinjaye wanda zai bashi damar ci gaba da mulki a wa’adi na 3, inda ya sha alwashin shigar da ‘yan adawa cikin gwamnatinsa don kwantar da hankulan jama’a.

Shugaba Alassane Ouattara yayin wani taro a birnin Abidjan.
Shugaba Alassane Ouattara yayin wani taro a birnin Abidjan. REUTERS/Luc Gnago/File Photo
Talla

Zaben wanda bangaren adawa ya kauracewa, ya gudana bayan tashe-tashen hankulan da yak ai ga kame tarin jama’a galibi wadanda ke adawa da matakin shugaban na sake tsayawa takara a karo na 3.

Shugaban hukumar zaben kasar Ibrahime Coulibaly ya ce Ouattara ya yi nasarar lashe kashi 94 na yawan kuri’un da aka kada ko da yake kashi 53 na yawan al’ummar kasar masu katin zabe ne kadai suka kada kuri’a a zaben.

Tun cikin watan Agusta Ivory Coast ke fuskantar zafafan zanga-zangar tare da gangamin nuna adawa da kuma bore ga Ouattara dai dai lokacin da tattalin arzikin kasar ke ci gaba da durkushewa.

Akwai dai fargabar dawowar makamancin rikicin kasar na shekaru 10 da suka gabata wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla dubu 3 a lokacin da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ya ki amincewa da sauka daga mulki duk da shan kaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.