An binne Pierre Buyoya a Mali
Buyoya wanda ya mutu a birnin Paris na Faransa saboda cutar corona, an yi jana’izarsa ne a birnin Bamako, wato birnin da ya shafe tsawon shekaru takwas yana jagorantar wani aiki na musamman a matsayin manzan Kungiyar Tarayyar Afrika.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin makusantansa sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, Buyoya ya mutu ne a 17 ga watan Disemban 2020.
Tun a farkon mako aka kwantar da shi a asibiti a birnin Bamako, kafin komawa da shi Paris, inda aka sanya masa na’urar da ke taimaka masa yin numfashi.
A yammacin jiya aka yi balaguro da shi zuwa Paris. Sai dai ya yi ban-kwana da duniya a daidai lokacin da motar daukar marasa lafiya ta kai shi asibiti don fara karbar magani.
A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne, Buyoya ya yi murabus daga kujerar manzan Kungiyar Tarayyar Afrika a Mali bayan kotu ta yi masa daurin rai da rai a Burundi bisa samun sa da hannu a kisan magajinsa a shekarar 1993.
Buyoya ya fara darewa kan kujerar shugabancin Burundi ne ta hanyar juyin mulkin 1987.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu