Isa ga babban shafi
Afrika-Burundi

Kotu ta umarci gaggauta rantsar da zababben shugaban Burundi

Kotun Fasalta kundin tsarin mulkin Burundi ta bada umurnin rantsar da zababben shugaban kasa Evariste Ndashimiye cikin gaggawa sakamakon mutuwar Pierre Nkurunziza wanda ya gamu da bugun zuciya.

Shugaban kasar Burundi mai jiran gado Évariste Ndayishimiye.
Shugaban kasar Burundi mai jiran gado Évariste Ndayishimiye. AFP
Talla

Mai baiwa shugaban kasar shawara Willy Nyamitwe ya ce kotun ta bada umurnin rantsar da zababben shugaban ba tare da bata lokaci ba, inda take cewa babu dalilin nada shugaban riko saboda ganin ana da zababben shugaban kasa.

Kundin tsarin mulkin Burundi ya amince da rantsar da shugaban Majalisar Dokoki ne idan shugaban kasa yam utu ko kuma ya gamu da wata matsalar da ba zata bashi damar gudanar da ayyukan sa ba, duk da yake kasar na da mataimakin shugaban kasa guda 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.