Isa ga babban shafi
Burundi

Al'ummar Burundi na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

An bude rumfunan zabe a Burundi domin bai wa al’ummar kasar damar kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki, da na kananan hukumomi, zaben da shugaba Pierre Nkurunziza ba zai tsaya takara ba.

Wata 'yar kasar Burundi, yayin kada kuri'a a zaben 'yan majalisun dokokin kasar, a yankin Kinama dake kusa da babban birnin kasar Bujumbura. 29/6/2015.
Wata 'yar kasar Burundi, yayin kada kuri'a a zaben 'yan majalisun dokokin kasar, a yankin Kinama dake kusa da babban birnin kasar Bujumbura. 29/6/2015. REUTERS/Paulo Nunes dos Santos
Talla

Tun da misalin karfe 6 na safe agogon kasar ne aka bude rumfunan zaben, inda ake sa ran mutane sama da milyan biyar za su fita domin kada kuri’unsu a wannan zabe mai cike da kalubale, lura da irin tashe-tashen hankulan da aka sama a 2015

Mutane 7 ne suka tsaya takara a zaben na yau, to sai dai hankula sun fi karkata ne ga Janar Evariste Ndayishimiye da ke samun goyon bayan shugaba mai barin gado, sai kuma Agathon Rwasa na babbar jam’iyyar adawa.

Hukumar zaben kasar ta samar da akwatuna kada kuri’a har guda uku a kowace rumfar zabe, domin bai wa jama’a damar bambanta yadda ake zaben shugaban kasa, ‘yan majalisa da kuma kananan hukumomi.

Burundi dai kasa ce da ta yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, domin ko a shekara ta 2015 sai dai aka samu asarar rayukan mutane sama da dubu daya yayin da wasu kusan dubu 400 suka bar gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.