Isa ga babban shafi
Burundi

Gwamnatin Burundi ta kori manyan jami'an hukumar WHO

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bakin ciki kan yadda gwamnatin Burundi ta kori masanan hukumar lafiyarta dake taimakawa kasar wajen yaki da annobar COVID-19, wadda ta kama mutane 27 a kasar ta kuma kashe mutuum guda.

Wasu 'yan kasar Burundi, yayin wanke hannayensu don samun kariya daga cutar coronavirus. 18/3/2020.
Wasu 'yan kasar Burundi, yayin wanke hannayensu don samun kariya daga cutar coronavirus. 18/3/2020. © AFP / Onesphore Nibigira
Talla

Gwamnatin Burundi ta baiwa jami’an Hukumar Lafiya ta Duniya umurnin ficewa daga cikin kasar ne saboda zargin da ake musu na katsalandan akan ayyukan da kasar keyi wajen tinkarar annobar COVID-19.

Wata wasika da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta rubutawa Hukumar ta bayyana cewar bata bukatar Babban jami’in hukumar, Dr Walter Kazadi Mulombo, da jami’in dake jagorancin yaki da annobar, Dr Jean Mulunda Nkata, da jami’in yaki da cututtuka masu yaduwa, Dr Ruhana Mirindi Bisimwa, da masanin kula da dakin gwajin cutar COVID-19, Farfesa Daniel Tarzy su cigaba da zama a cikin Burundi.

Wasikar ba tayi Karin haske kan zargin da ake yiwa jami’an ba, amma majiyoyin diflomasiya sun ce tun a watan jiya gwamnatin kasar ke kokarin korar jami’an.

Cibiyar yaki da cututtuka na kasashen Afirka ta bayyana takaicin daukar matakin, yayin da ita ma Hukumar Lafiya ta bayyana damuwa kan lamarin.

Korar wadanan jami’ai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa da na Yan Majalisu a karshen wannan makon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.