Isa ga babban shafi
Burundi

MDD ta gargadi Shugaban Burundi da kada ya nemi wa'adin mulki na hudu

Babban Sakatare Janar na MDD Antonio Gutteres ya gargadi shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza da kada ya nemi zarcewa da iko waadi na hudu, gudun kada ya tsoma kasar sa cikin rudani.

Shugaban Burundi  Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

Wani rahoto da kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya gano na cewa Babban Sakataren MDD ya damu matuka gameda ikirarin shugaban na Burundi wanda yake rike da madafun iko tun shekara ta 2005.

Gutteres ya fadawa komitin Sulhu na MDD cewa yunkurin zarcewa da Shugaba Nkurunziza ke yi na da hatsarin gaske.

Daruruwan mutanen kasar ne dai suka rasa rayukansu a lokacin da Shugaban ya nace da zarcewa wa'adi na uku wanda tsarin mulkin kasar ya ki amincewa da hakan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.