An kashe Ministan muhalli a Burundi
Wasu ‘yan bindiga sun kashe ministan kare muhalli na Burundi Emmanuel Niyonkuru a birnin Bujumbura. Wanda wannan ne karon farko da aka kashe wani babban jami’in gwamnati bayan kasar ta fada cikin rudanin siyasa.
Wallafawa ranar:
Kakakin ma’aikatar ‘yan sanda Pierre Nkurikiye, ya ce an harbe ministan ne a hanyarsa ta zuwa gida bayan kammala bukin shiga sabuwar shekara.
Kisan na zuwa bayan shugaban kasar Pierre Nkunrunziza ya sanar da aniyar sake gyara kundin tsarin mulki domin bas hi damar neman wa’adi na hudu a 2020, duk an samu lafawar rikici bayan ya zarce a wa’adi na uku.
Rundunar ‘Yan sandan kasar ta sanar da cafke wata mata da ake zargi tana da hannu a harin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu