Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Dakarun Faransa sun hallaka 'yan ta'adda 30 a Mali

Dakarun kasar Faransa da ke yaki da ta'addanci karkashin rundunar Barkhane ta sanar da hallaka 'yan ta’adda sama da 30 a wasu hare haren da ta kai a kan iyakar Mali.

Dakarun rundunar Barkhane mai yaki da ta'addanci a kasashen Mali, Nijar, Burkina Faso da Mauritania.
Dakarun rundunar Barkhane mai yaki da ta'addanci a kasashen Mali, Nijar, Burkina Faso da Mauritania. RFI/Coralie Pierret
Talla

Sanarwar da rundunar ta gabatar, ya nuna cewar tsakanin 6 zuwa 7 ga wannan watan, dakarun rundunar sun kai hare hare a Yankin Liptako-Gourma da ke iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar wanda ya bada damar kashe 'yan ta’adda 20 da kuma lalata motoci da dama.

Mai Magana da yawun sojin Kanar Frederic Barbry ya ce sun yi amfani da jirgin sama mai sarrafa kan sa da jirgin saman soji wajen kai hare haren.

Rundunar ta kuma sanar da raba wasu mayakan sama da 24 da makamai a Yankin Sahara, ba tare da bayani kan wadanda ta kama ba.

Gwamnatin Faransa ta sanar da kara yawan dakarun ta a yankin Sahel daga 4,500 zuwa 5,100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.