Isa ga babban shafi
DR Congo

An dage zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Congo

Hukumar Zaben Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta dage zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi mai zuwa. Hukumar ta CENI ta gana da ‘yan takara a zaben, in da ta shaida musu cewa, ba za ta iya gudanar da zaben ba sakamakon matsalar da ke tattare da kayayyakin kada kuri’u.

Hukumar zaben CENI ta ce, an dage zaben ne saboda matsalar kayan aiki
Hukumar zaben CENI ta ce, an dage zaben ne saboda matsalar kayan aiki Patient Ligodi / RFI
Talla

Theodore Ngoy, daya daga cikin ‘yan takara 21 da Hukumar zaben da gana da su a zauren Majalisar Dokokin Kasar a wannan Alhamis, ya sanar da manema labarai cewa, shugaban hukumar, Corneille Nangaa ya shaida musu cewa, ba za su iya gudanar da zaben ba sakamakon matsalar kayan aiki.

Gabanin matakin dagewar, al’ummar kasar ta zura ido domin ganin wanda zai gaji shugaba Joseph Kabila wanda ya shafe tsawon shekaru 18 akan karagar mulki, yayin da ake kallon wannan zaben a matsayin irinsa na farko da zai kai ga mika mulki a demokradiyance.

Yanzu haka, babu masaniya game da sabon jadawalin zaben, yayin da wani dan takara Martin Fayulu ke cewa, ba za su amince da jinkirta zaben ba bayan tsawon lokacin da aka dauka ana dakonsa.

Wannan dai na zuwa ne bayan gobara ta tashi a ofishin hukumar zaben, abin da ya lalata kashi 80 cikin 100 na na’urorin kada kuri’u a birnin Kinshasa a cewar hukumar ta CENI.

Ana daririn kadar ta tsunduma cikin wani sabon tashin hankalin sakamakon dage zaben na ranar 23 ga watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.