Isa ga babban shafi
DRC

'Yan bindiga sun kai hari a rumbun ajiyar kayayyakin zabe

Yayin da ya rage kwanaki kadan a gudanar da zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, rundunar tsaron kasar ta ce,  wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kan rumbun ajiye kayayyakin hukumar zaben kasar da ke yankin Beni a gabashin kasar a karshen mako.

Nau'ukan kayayyakin zabe a Jamhuriyar Congo
Nau'ukan kayayyakin zabe a Jamhuriyar Congo John WESSELS / AFP
Talla

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar ya ce, ga alama maharan magoya bayan wata kungiyar ‘yan tawaye ne, to amma sojoji da kuma ‘yan sanda sun murkushe yunkurinsu na kona rumbun ajiye kayayyakin zaben.

Shugaban hukumar zabe a lardin na Beni Deogratias Mbayahi ya ce, akwai na’urorin tantance masu kada kuri’a sama da dubu biyu da sauran kayayyyakin zabe a cikin wannan rumbu da ‘yan tawayen suka yi yunkurin kai wa harin.

A daren Laraba zuwa wayewar garin Alhamis na makon jiya, wani rumbun hukumar zaben ya kone tare da lalata kashi 80% na kayayyakin da ya kamata a yi amfani da su a birnin Kinshasa.

Ministan Cikin Gidan kasar Henri Mova ya ce, lura da halin da ake ciki abu ne mai yiyuwa gwamnati ta yi amfani da sojoji domin gudanar da wasu ayyukan da ya kamata ‘yan sanda su yi a lokacin zaben wanda aka tsara gudanarwa a ranar 23 ga wannan wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.