Tarin jama'a sun jikkata a arangama tsakanin bangarorin adawar Congo
Wasu Majiyoyi a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun ce akalla mutum guda ya mutu, yayin da wasu sama da 80 suka samu raunuka, sakamakon arangamar da aka yi tsakanin magoya bayan jam’iyyun daban daban a zabe mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne a Tshikapa da ke Yankin Kasai, lokacin da jiragen manyan 'yan siyasa biyu, Felix Tshesekedi da ministan ilimi Maker Mwangu suka sauka.
A baya-bayan nan ana yawan samun barkewar rikici musamman tsakanin bangarorin adawa a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo wanda a lokuta da dama kan kai ga asarar rayuka, yayinda a bangare guda hare-haren 'yan bindiga ke kara ta'azzara.
Kasar Congo na shirin gudanar da zaben shugaban kasa a karshen wannan mako, wanda ake saran ganin an zabi wanda zai maye gurbin shugaba Joseph Kabila da ya kwashe shekaru 17 a karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu