Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo - Zabe

Mai yiwuwa Jamhuriyyar Congo ta dage zaben kasar na makon nan

Wasu rahotanni daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo na nuni da cewa akwai yiwuwar dage zaben kasar da aka shirya gudanarwa ranar lahadin karshen makon nan.

Shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Joseph Kabila.
Shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Joseph Kabila. JOHN WESSELS / AFP
Talla

Wani jami`in hukumar CENI mai kula da harkokin zabe a kasar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa mataki yanzu haka ana tattaunawa kan batun wanda akwai yiwuwar nan gaba kadan a sanar da matsaya akai.

A cewar Jami`in matakin baya rasa nasaba da gobarar da ta kone wasu daga cikin na`urori da takardun zaben da aka shirya amfani da su a Kinshasa babban birnin kasar.

Wannan dai ne zabe karon farko na shugaban kasa da `yan majalisu da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo za ta gudanar wanda ake fatan ya kawo gagarumin sauyi a tsarin gudanarwar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.