An kara kashe wani dan Najeriya a Afrika ta kudu
Al’ummar Najeriya mazauna Afrika ta kudu sun tabbatar da kone wani dan Najeriya Clement Nwaogu wanda aka bankawa wuta da ransa har ya mutu a hare-haren kin jinin baki da ‘yan Afrika ta kudun ke ci gaba da kai wa kan baki mazauna kasar.
Wallafawa ranar:
Da ya ke tabbatar da hakan ga kamfanin dillacin labaran Najeriyar NAN, Habib Miller sakataren yada labaran kungiyar ‘yan Najeriyar mazauna Afrika ta kudu, ya ce lamarin ya faru ne a yankin arewa maso yammacin Rustenburg inda maharan suka far masa da muggan makamai kafin daga bisani su banka masa wuta.
Wasu shaidun gani da Ido a cewar Mr Habib sun ce sai da Clement ya nemi daukin jami’an ‘yansandan kasar amma suka ki agaza mishi.
Tsawon lokaci kenan dai wasu tsageru a kasar ta Afrika ta kudu ke aiwatar da kisan gillar kan ‘yan Najeriya ba kuma tare da daukar wasu kwararan matakai daga gwamnatocin kasashen biyu don dakatar da su ba.
A cewar Mr Miller har yanzu akwai ‘yan Najeriyar 14 da jami’an ‘yansandan Afrika ta kudun ke rike da su sakamakon zanga-zangar adawa da kisan da ake musu da suka yi a watan Fabarairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu