Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Rikicin siyasa ya barke a Afrika ta Kudu

Rahotanni daga Afirka ta kudu sun ce an samu tashin hankali a kasar, inda matasa suka rika cinna wa motoci wuta tare da rufe hanyoyi suna kona tayun mota saboda zaben kananan hukumomin kasar da za ayi.

Matasan afrika ta Kudu tana cinna wa motoci wuta tare da kona tayu a kan hanyoyi saboda zaben kananan hukumomi mai zuwa
Matasan afrika ta Kudu tana cinna wa motoci wuta tare da kona tayu a kan hanyoyi saboda zaben kananan hukumomi mai zuwa REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Bayanai sun nuna cewar tashin hankalin ya biyo bayan rahsin jituwar da aka samu wajen tsayar da dan takaran kujerar shugabancin magajin garin Pretoria a zaben da za ayi a ranar 3 ga watan Agusta mai zuwa.

Magoya bayan jam’iyyar ANC mai mulkin kasar sun tare babbar hanyar da ta tashi daga arewa zuwa kudancin kasar da ake kira N1, inda suka rika ruwan duwatsu kan motocin da ke zirga zirga.

Sakatare Janar na Jam’iyyar, Gwede Mantashe ya zargi 'yan bangan siyasa da tayar da hankalin don goyan bayan masu basu na goro, amma kuma su masu zanga -zangar sun zargi jam’iyyar ce da dauki dora, maimakon wanda jama’a ke so.

Ko a kwanakin baya saida  aka gudanar da irin wannan zanga-zangar a Durban, Yankin da shugaba Jacob Zuma ya fito.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.