Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An dambace tsakanin ‘yan majalisa da jami’an tsaro a Afirka ta Kudu

An bai wa hamatta iska tsakanin ‘yan majalisar dokoki na bangaren adawa da kuma jami’an tsaron kasar Afirka ta Kudu a yau talata, lokacin da ake kokarin fitar da ‘yan adawar daga cikin zauren majalisar.

Rikici a Majalisar Dokokin Afrika ta Kudu
Rikici a Majalisar Dokokin Afrika ta Kudu AFP
Talla

Wasu ‘yan majalisar 20 daga bangaren adawa ne suka kece da ihu a lokacin da shugaba Jacob Zuma ke gabatar da jawabi, lamarin da ya sa jami’an tsaro yin amfani da karfi domin fitar da su, toh daga nan ne aka fara dambe a tsakaninsu.

Shugaba Jacob Zuma na ci gaba da fuskantar matsin lamba na yayi murabus daga mukaminsa tun bayan badakalar yin anfani da kudadden gwamnati wajen kawata muhallinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.