Isa ga babban shafi
South Africa

Shugaban Africa Ta Kudu Jacob Zuma Ya Tsallake Tsigewa

Majalisar Dokokin kasar Africa ta Kudu ta gaza zartas da tsige Shugaban kasar Jacob Zuma wanda  wata kotun Tsarin mulkin kasar ta ce ya saba kundin tsarin mulkin.

Shugaba Jacob Zuma na Kasar Africa ta Kudu.
Shugaba Jacob Zuma na Kasar Africa ta Kudu. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Wakilan majalisar daga jamiyyar dake mulki, ANC sun goyi bayan Shugaban kasar a jefa kuria'r da aka yi da babban rinjaye na kuriu 233 yayin da wakilai 143 suka nemi a tsige shi.

Kotun tsarin mulki a makon jiya ta zargi shugaban kasar da aikata ba daidai ba saboda amfani da dukiyar Gwamnati wajen gyatta wani gida daya mallaka.

Shugaban jamiyyar adawa ta Democratic Alliance Mmusi Maimane ya fadawa majalisar cewa cin hanci da rashawa ta mamaye jamiyyar dake mulkin kasar ANC.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.