Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Jacob Zuma ya bukaci a kawo karshen kai wa baki hari

Shugaban kasar Africa ta kudu Jacob Zuma ya roki al’ummar kasar da su kawo karshen kai hare-hare kan ‘yan kasashen waje, al’amarin da ya zuwa yanzu ya kai ga kashe baki akalla shida, lamarin da ke cigaba da bazuwa a sassan kasar

Shugaban Kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma
Shugaban Kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Cikin makonni biyu da suka gabata dai shaguna da gidaje, mallakin ‘yan kasar Somalia, Habasha, da Malawi da ke garin Durban da kuma wasu garuruwa da ke kusa sun sha ta’adi daga ‘yan kasar, lamarin daya tilastawa dangi da iyalan ‘yan kasasahen waje tserewa zuwa wasu sansanoni da ake gadin su.

Haka nan kuma shagunan wasu baki da ke yankunan Jeppestown a Johanneswburg an kai masu hari cikin dare, yayin da ‘yan sanda ke amfani da barkonun tsohuwa don tarwatsa masu borin

Shugaba Jacob Zuma ya fadawa majalisar kasar a Cape Town cewa nuna kyamar bakin ba abinda zasu amince dashi bane.

Zuma, Yace babu wani dalili da zai sa a rika kaiwa baki hare hare, ana fasa musu shagunan da kuma kwasan ganima.

Shugaba Zuma ya kuma bada tabbacin cewar an umarci jami’an tsaro da su kare jama’a, sannan kuma akama dukkan wanda aka gani yana neman tada zaune tsaye.
 

A shekarar ta 2008 mutane 62 aka kasha a irin wannan harin
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.