Isa ga babban shafi
Burundi

'Yan adawa a Burundi sun yi watsi da shirin yi wa tsarin mulki kwaskwarima

Jam’iyyun adawa a kasar Burundi sun yi watsi da abinda suka kira shirin tilastawa ‘yan kasar kada kuri’a a zaben raba gardama da gwamnati  ta shirya  gudanarwa a watan Mayu mai zuwa.

Masu zanga-zanga a  Burindi rike da tutotin kasar, yayin wata gangamin adawa ta manufofin gwamnati a Bujumbura
Masu zanga-zanga a Burindi rike da tutotin kasar, yayin wata gangamin adawa ta manufofin gwamnati a Bujumbura Reuters/G. Tomasevic
Talla

Jam’iyyun adawar sun lashi takobin kalubalantar zaben raba gardamar kan sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasar, wanda zai bai wa shugaba mai ci, Pierre Nkrunziza damar ci gaba da shugabanci zuwa shekarar 2034.

A farkon makon da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan Burundi ta yi gargadin cewa zata garkame duk wani dan kasar da ya yi kokarin gudanar da zanga-zangar adawa da shirin kada kuri’ar raba gardama kan sauya kundin tsarin mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.