Cacar-baki ta kaure game da sakamakon zaɓen Kenya
Sama da mutane 90 ne suka mutu a tashin-tashinar da ke da alaƙa da zaɓen, inda aka zargi ƴansandan ƙasar ta Kenya da aikata akasarin kashe-kashen.
Wallafawa ranar:
Ƙungiyar tarrayar Turai ta bakin shugaban tawagar masu sa ido a zaɓen na Kenya Marietje Schake, ta bayyana zaɓen shugabancin ƙasar da ya gabata a matsayin zaɓen da ke cike da kura-karai.
Rahoton wanda aka fitar a Brussels na ƙasar Belgium a maimakon ƙasar ta Kenya, ya yi kakkausar suka a kan sakamakon zaɓen.
Sai dai ƙasar ta Kenya ta bakin Jakadanta da ke Belgium, Johnson Weru, ta la’anci sanarwar daga masu sa ido a zaɓen, tare da cewa hakan na iya haifar da rikici a ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu