Isa ga babban shafi
Kenya

Zaben Kenya: 'Yan sanda sun hallaka mutum Uku

Akalla mutum Uku aka tabbatar da mutuwarsu a munanan tashin hankulan da aka samu a wasu mazabu da ke Kenya wajen gudanar da zaben shugaban kasa.

'Yan sanda sun cafke daya daga cikin masu Zanga-zanga
'Yan sanda sun cafke daya daga cikin masu Zanga-zanga REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Yanzu dai an dage zaben yankunan 4 da suka hada da Homa Bay da Kisumu da Migori da Siaya inda aka samu tashin hankali.

Rahotanni ‘yan sanda da majiyoyin asibiti, sun ce an kashe mutumin farko a wata mazaba da ke Nairobi, lokacin da masu zanga-zangar suka yi kokari datse zaben da shugaban ‘yan adawa Raila Odinga ya kauracewa.

Sanarwar da ‘yan sanda kasar suka fitar mai dauke da sa hannu mataimakin Sufeta janar George Kinoti, ta ce jami’an tsaro sunyi harbin bindiga ne domin kare kansu daga masu zanga-zangar da ke kokarin kai musu hari.

Daga watan Agusta da ya gabata lokacin soke zaben farko zuwa yanzu akalla mutane 43 aka hallaka. Wanda kungiyoyin kare hakkin bil’adama ke cewa aksari ‘yan sanda ke harbe su.

Yanzu dai an dakatar da zaben a wasu yankunan 4 zuwa ranar Assabar kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Shugaban hukumar, Wafula Chebukati, ya ce dage zaben ya zama dole la’akari da kalubalin tsaro da aka fuskanta wanda har ya kai ga rasa rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.