Zaben Kenya: Kasashen yammaci na Fargaba
Jakadun kasashen Yammacin Duniya a birnin Nairobi na Kenya, sun bayyana furgbansu dangane da halin da kasar Kenya za ta iya fadawa sakamakon yadda lamurra suka zafafa kafin zaben shugabancin kasar na jibi alhamis.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jakadan Amurka Robert Godec wanda ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitar da sanarwar hadin-gwiwa da jakadun suka fitar a jiya litinin, ya ce alhaki ya rataya a wuyan ‘yan siyasa domin su kwantar da hankulan magoya bayansu domin kaucewa rikici a lokacin zaben.
Shugaban 'yan adawa da ya janye takararsa Raila Odinga ya yi barazanar kaddamar da zanga-zanga a ranar zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu