Isa ga babban shafi
Najeriya

“A Chibok ya kamata a yi ihun dawo da ‘yan matan da aka sace”

Yau 14 ga watan Afrilu shekaru uku kenan cur da ‘yan Boko Haram suka kai hari tare da yin awon gaba da ‘yan mata 276 a makarantar Sakandaren garin Chibok da ke jihar Bornon Najeriya.

Kungiyar BringBackOurGirls (#BBOG) da ke fafutikar ganin an sako 'yan matan Chibok a Najeriya
Kungiyar BringBackOurGirls (#BBOG) da ke fafutikar ganin an sako 'yan matan Chibok a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shekaru uku da faruwar lamarin, har yanzu akwai sauran ‘yan mata 195 da ke ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan kungtiyar ta Boko Haram bayan kubutar da wasu daga cikinsu.

Amma a yayin da gungun kungiyoyin da ke fafutukar ganin an sako sauran ‘yan matan wato BringBackOurGirls ke shirin gudanar da taron gangami domin tunawa da ranar, Farfesa Hauwa Biu daya daga cikin shugabannin da ke gwagwarmaya a Borno, na ganin cewa bai kamata a takaita kan batun ‘yan matan Chibok kawai ba domin akwai mutane da dama da Boko Haram ke garkuwa da su.

Farfesa Hauwa Biu ta kalubalanci ‘Yan BringBackOurGirls su dawo Chibok idan da gaske su ke yi.

“Idan a Abuja za a tsaya ana gwagwarmaya bai kamata a ce an takaita kawai kan ‘yan Matan Chibok ba”, a cewar Farfesa Biu.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana tattaunawa da ‘yan Boko Haram tare da shiga tsakanin kungiyar agaji ta Red Cross domin kubutar da ‘yan matan na Chibok.

A watan Oktoban bara, an kubutar da wasu daga cikin matan su 21 ta hanyar shiga tsakanin wakilan gwamnatin Switzerland da kungiyar agaji ta Red Cross.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.