Shugaba Buhari na Najeriya ya nanata burin kubutar da 'yan matan Chibok daga hannun Boko Haram
Yayin da ‘yan matar Chibok ke cika shekaru uku hannun 'yan Boko Haram, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nanata burin Gwamnatinsa na ganin sun kwato sauran matan da aka sace daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.
Wallafawa ranar:
Juma'a 14 ga watan Aprilu na shekara ta 2014 ne ‘yan matan na Chibok ke cika shekaru uku da sace su daga makarantar Sakandare dake garin Chibok a Jihar Borno.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbo ‘yan mata fiye da 20 daga cikin ‘yan mata 270 da aka sace.
Shugaban Najeriya ya bayyana cewa Gwamnati na tattaunawa da ‘yan Boko Haram tare da taimakon wasu kungiyoyi daga ciki da wajen Najeriya domin ganin an sako ‘yan matan ba tare da an yi masu lahani ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu