Amurka ta sake tallafa wa yankin tafkin Chadi
Gwamnatin Amurka ta sake ware Dala miliyan 92 don tallafa wa wadanda ke fama da matsaloli saboda rikice-rikice da karancin abinci a Najeriya da kuma kasashen yankin tafkin Chadi.
Wallafawa ranar:
Wadanda za su ci gaciyar tallafin sun hada da masu fama da rikicin Boko Haram musamman ‘yan gudun hijira da ke samun mafaka a sansanoni daban-daban.
Za a yi amfani da kudaden wajen samar da abinci da ruwan sha da matsugunai da kuma magunguna ga mabukatan.
Sama da mutane miliyan 6 ne cikin bukatar abinci da gaggawa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi sakamakon halin da rikicin Boko Haram ya jefa su a ciki.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, ana bukatar tallafin Dala biliyan 1 nan da shekara mai zuwa don biyan bukatun wadannan mutanen da ke fama da matsalolin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu