Mutane milyan biyar ne ke bukatar tallafi a arewa maso gabashin Najeriya
MDD ta ce ana bukatar sama da dala milyan dubu daya a shekara mai zuwa domin taimakawa jama’ar da ke fama da matsaloli sakamakon rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan jinkai na na MDD Peter Lundberg, ya bayyana a wata sanarwa cewa akalla mutane milyan 5 ne za su kasance a cikin hali na bukata cikin shekara mai kamawaa yankin tare da yin kira ga kasashen duniya da kuma masu zaman kansu domin taimakawa.
Sanarwar ta bayyana jihohin Borno, Yobe da Adamawa a matsayin wadanda ke cikin hali na bukatar samun taimako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu