Isa ga babban shafi
Kamaru

Boko Haram ta kashe sojojin Kamaru 6

Kungiyar Boko Haram ta kai wani kazamin hari kan sansanin sojin hadin-kai na kasashen tafkin Chadi da ke tsibirin Darak, inda ta kashe sojojin kasar Kamaru guda 6.

Sojojin Kamaru da ke fada da Kungiyar Boko Haram ta Najeriya
Sojojin Kamaru da ke fada da Kungiyar Boko Haram ta Najeriya RFI/OR
Talla

Rahotanni sun ce, akwai daya daga cikin ‘yan kungiyoyin sa-kai da ke taimakawa jami’an tsaron da aka kashe a harin.

Wannan na zuwa a yayin jami’an tsaro a Kolofata suka harbe wani da ke kokarin kai harin kunar bakin wake kusa da inda soji ke binciken ababan hawa akan iyaka da Najeriya.

Sojojin Kamaru na cikin rundunar hadin guiwa ta kasashen Chadi da Nijar da Najeriya da kuma Benin da ke fada da mayakan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.