Kamaru-Boko Haram
Hare-haren Boko Haram ya yi sauki a Kamaru-ICG
Wata Kungiyar da ke sa ido kan rikice rikice a duniya, wato International Crisis Group, ta ce hare haren kungiyar Boko Haram ya yi sauki sosai a kasar Kamaru sakamakon nasarorin da jami’an tsaron kasar ke samu.
Wallafawa ranar:
Talla
Mai Magana da yawun kungiyar Hans De Marie Heungoup, ya ce watannin da suka gabata jami’an tsaron sun yi nasara dakile duk wani hari da kungiyar ke yi, sabanin yadda abin ya ke shekaru biyu da suka gabata.
Tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015 akalla mayakan Boko Haram 1,000 suka addabi arewacin Kamaru da hare hare.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu