Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ce ta Uku a fuskantar hare-haren ta'addanci a duniya

Cibiyar bincike kan samar da zaman lafiya da kuma tattalin arziki, GTI, ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta uku, cikin jerin kasashen duniya da suka fi fuskantar hare-haren ta’addanci.

Babban hafsan sojin kasan Najeriya, Tukur Buratai
Babban hafsan sojin kasan Najeriya, Tukur Buratai AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Rahoton cibiyar na kunshe ne cikin wani bincike da ta gudanar kan tasirin ta’addanci a kasashen Duniya 163, da ke wakiltar kasha 99% na al’ummar Duniya.

Sai dai kuma duk da wannan matsayi da Najeriya ta tsinci kanta, Rahoton Cibiyar ta, GTI, da ke da ofisoshi a biranen Sydney da NewYork, ya ce an samu raguwar mutanen da mayakan Boko Haram ke kashewa a Najeriya da kashi 34 cikin 100, idan aka kwatanta da kashe kashen kungiyar a shekarar 2015.

Rahoton ya ce an samu raguwar mutane sama da 6100 a shekara ta 2014 da mayakan Boko Haram suka kashe, zuwa mutane 4095 a shekara ta 2015.

Kasashe 10 na farko da Cibiyar binciken kan zaman lafiyar ta ce sune mafi hadarin zama a Duniya sun hada da Iraqi da Afghanistan da Najeriya da Pakistan da Syria.

Sai kuma kasashen Yemen da Somalia da India, yayin da kasashen Masar da Libya ke a matsayi na tara da kuma goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.