Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta hallaka mutane 22 a Munguno

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a wasu kauyukan da ke karamar hukumar Monguno a jahar Borno inda suka hallaka mutane 22.

Wani hari da Boko Haram suka kai a garin Benisheik a Jahar Borno a Najeriya
Wani hari da Boko Haram suka kai a garin Benisheik a Jahar Borno a Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Rahotanni da ke fitowa daga kasar na cewa an kai harin ne tun ranakun litinin da talata amman sai yau labarin harin ke fitowa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke cewa, ta na tattaunawa da wakilan kungiyar don sako ‘yan matan sakandaren Chibok fiye da dari biyu da Boko Haram din ta sace a shekarar 2014.

Munguno na daga cikin garuruwan jahar Borno da Boko Haram ta kwace kafin sojin Najeriya su sake kwato ta daga kungiyar.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu dari biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.