Isa ga babban shafi
Mali

Tsoffin yan tawayen Mali za su kauracewa zaben wakilan hukumomi na gobe

A jiya juma’a ne aka kawo karshen yakin neman zaben wakilan kananan hukumomin a kasar.Gwamnatin kasar ta bayyana cewa tana a shirye donin gani komi ya kamala kama daga jami’an tsaro dama akwatinan zabe . 

Hotunan wasu yan takara a Bamako dake babban birnin kasar Mali
Hotunan wasu yan takara a Bamako dake babban birnin kasar Mali Habibou KOUYATE / AFP
Talla

Gungun jam’iyyoyin adawa na kasar na cigaba da bayyana damuwa kan abinda suka kira shirya zabe cikin rudani, yayinda a daya wajen kungiyar tsoffin yan tawayen arewacin Mali suka bukaci magoya bayan su da su kauracewa zaben ranar lahadi 20 ga wannan watan da muke cikin sa .

Karo na farko tun bayan hawan karagar mulkin Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita a shekara ta 2013 da kasar Mali ke shirya zaben wakilan kananan hukumomi tun bayan da arewacin kasar ya fada hannun yan tawaye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.