Zanga zangar iyalan sojojin da suka mutu a Mali
A kasar Mali, iyalan Sojoji 21 da aka gano gawawakin su a wani rame dake yankin Diago kusa da Bamako babban birnin kasar a watan Disemba na shekara ta 2013 sun bukaci hukumomin kasar da su gaggauta kamala bicinke a kai.Ana dai zargin tsohon Shugaban mulkin sojin kaftain Sanogo da mutanen sa wajen aikata wannan kazamin aiki.
Wallafawa ranar:
An dai kashe wadannan sojojin ne bisa laifin cewa sun shirya kiffar da mulkin kaftain Amadou Sanogo, indan kuma aka yi tuni ranar 27 ga watan Novemba shekarar 2013 ne kotu a Mali ta zargi Kaftain Sanogo da wasu mukaranba sa da aikata kisan wadannan sojojin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu