Isa ga babban shafi
Mali

‘Yan tawayen Mali sun tsagaita buda wuta

Shugaban Kungiyar ‘Yan Tawayen Mali ta Ansaruddine Iyad Ag Ghaly ya sanar da tsagaita buda wuta a hare haren da suke kai wa kan fararen hula da sojojin kasar da kuma dakarun samar da zaman lafiya.

Iyad ag Ghali, Shugaban Kungiyar Ansar Dine ta Mali
Iyad ag Ghali, Shugaban Kungiyar Ansar Dine ta Mali AFP PHOTO / ROMARIC OLLO HIEN
Talla

Shugaban kungiyar Musulman Mali, Mahmoud Dicko ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar ya samu sako daga Ag Ghaly wanda ya tabbatar da dakatar da kai hare haren.

Kungiyar Ansaruddine ta dade tana kai munanan hare hare cikin kasar tun lokacin da Sojoji suka kifar da gwamnatin Toumani Toure inda ‘Yan tawayen suka samu nasarar kwace yankin arewacin Mali.

Mahmoud Dicko ya ce ya samu wasikar daga shugaban ‘Yan tawayen a watan Satumba domin bude kofar hawa teburin sulhu.

Sai dai gwamnatin Mali na shakku akan ikirarin na ‘Yan tawayen wadanda ke ci gaba da kai hare hare a cikin kasar.

Tun a 1990 Iyad Ag Ghaly, ke jagorantar ‘Yan tawayen abzinawa, wanda Amurka ta jefa cikin sunayen ‘Yan ta’adda da ke da alaka da kungiyar Al Qaeda reshen Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.