Isa ga babban shafi
Somalia

Tsohon Dan Majalisa ya kai hari a Somalia

Kungiyar Al Shabaab a Somalia, ta ce daya daga cikin mutanen da suka kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 a kusa da ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Mogadishiu, wani tsohon dan majalisar dokokin kasar ne da ya shiga ayyukan ta’addanci.

Dan Majalisar Salah Badbado bayan kammala aikin Majalisa ya sanar da shiga kungiyar Al Shebaab
Dan Majalisar Salah Badbado bayan kammala aikin Majalisa ya sanar da shiga kungiyar Al Shebaab REUTERS
Talla

Sanarwar da Al shabaab ta fitar ta ce dan majalisar mai suna Salah Badbado mai shekaru 53 ya shiga kungiyar ne bayan ya kammala aiki a majalisa tsakanin 2004 zuwa 2010.

An kai harin kunar bakin waken ne a jiya Talata, kusa da tashar jirgin sama na Mogadishu.

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afrika dukkaninsu sun yi allawadai da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.