Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND na tattaunawa da gwamnatin Buhari

Kungiyar tsoffin Tsagerun Naija Delta ta MEND da ta jima tana fasa bututun mai a Najeriya ta tabbatar da cewar tana tattaunawa da gwamnatin Muhammadu Buhari domin kawo karshen haren-haren da ake wa a kudancin kasar mai arzikin fetir.

Tsagerun Naija Delta sun jima suna kai hari a bututun mai a Najeriya
Tsagerun Naija Delta sun jima suna kai hari a bututun mai a Najeriya AFP
Talla

A sanarwar da kungiyar ta rabawa manema labarai, ta ce akwai tattaunawar da suka soma tsakanin wakilanta da jami’an tsaron da ke wakiltar gwamnatin Najeriya.

A kwanakin baya dai Ministan Wasanni da Matasa Barista Solomon Dalung ya ce ya zanta da tsagerun domin jin bukatunsu don kawo karshen tashin hankalin da ake samu a yankin Niger Delta.

MEND ta ce tana fatar tattaunawar zata taimaka wajen samo hanyar warware rikicin yankin.

A makon jiya, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewar kamfanonin mai na tattaunawa da tsagerun a madadin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.