Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya na ganawa da Avengers

Shugaba Muhamamdu Buhari ya sanar cewar gwamnatin sa na tattaunawa da tsagerun Naija Delta dake ci gaba da fasa bututun mai da zummar shawo kan matsalar dake kokarin durkusar da tattalin arzikin Najeriya.

'Yan tsagerun Niger Delta na barazana ga tattallin arzikin Najeriya
'Yan tsagerun Niger Delta na barazana ga tattallin arzikin Najeriya (Photo : AFP)
Talla

Shugaban yace gwamnatin na nazarin shirin yin ahuwa ga tsagerun wajen basu kudi da koya musu aikin yi da kuma samar da tsaro a Yankin.

Sai dai a bangare daya kungiyar Naija Delta Avengers kamar yadda aka saba ta fitar da sanarwar cewar bata da labara wata tattaunawar da ake.

Mai Magana da yawun kungiyar Birgediya Janar Mudoch Agbinibo yace idan zasu tattauna da gwamnati dole sai an samu wakilan kasashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.