Avengers sun kai hari bayan musanta ganawa da Dalung
Tsagerun kungiyar Niger Delta Avengers, NDA da ke kudancin Najeriya sun kaddamar da sabbin farmaki guda biyu, inda suka tarwatsa bututun man fetir na wani kamfanin mai a kusa da yankin Batan da ke jihar Delta.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce, an kai harin ne a jiya Litinin da misalin karfe 12 na rana agogon kasar kuma hakan na zuwa ne bayan kungiyar ta Avengers ta musanta tattaunawa da Ministan wasanni da matasa Barista Solomon Dalung don dakatar da kai hare-hare kan kadarorin gwamnati da ke yankinsu.
Kungiyar ta ce, Ministan ya gana da wasu ‘yan damfara ne amma ba mambobinta ba kamar yadda ya shaida wa maneman labarai.
A bangare guda, wata kungiyar tsagerun daban mai suna Niger Delta Suicides, NDS ta gargadi cewa, za ta gurgunta tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyi da dama matukar gwamnatin tarayya ta gaza samar da kyakkyawan yanayi domin tattaunawa da tsagarun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu