Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari ya sake gargadin tsagerun Niger Delta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ja kunnen tsagerun yankin Nija Delta da su rungumi sasantawa da gwamnati domin a cewarsa gwamnati a shirye ta ke ta dauki kowane irin mataki wajen ganin ta tabbatar da dorewar Najeriya a matsayin kasa daya al’umma daya.

Tsoffin mayakan MEND a yankin Niger Delta a 2008
Tsoffin mayakan MEND a yankin Niger Delta a 2008 (Photo : AFP)
Talla

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar shuwagabannin Addinai a karkashin jagorancin mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbanjo a wani shirin gaisuwar Sallah da suka kai a wannan laraba.

Har ila yau shugaba Buhari ya sake jan kunnen wadanda ake zargi da yin rub-da-ciki da dukiyar al’umma da su yi kokarin dawo da ita cikin girma da arziki kafin gwamnatin ta fuskance su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.