Isa ga babban shafi
Najeriya

An cakfe mutane shida da ake zargi da hannu a harin Nembe

Jami’an tsaron Najeriya sun sanar da kama mutane shida da suke zargi da hannu wajen kai hari a barikin sojan Nembe da ke jihar Bayelsa yankin Niger Delta a makon da ya gabata.

Mayakan Mend a cikin shirin fada, ranar 17 ga watan satumbar 2008.
Mayakan Mend a cikin shirin fada, ranar 17 ga watan satumbar 2008. (Photo : AFP)
Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa Asinim Butswat, ya ce an kama ‘yan fashi akan ruwa su 6 wadanda ake zargin cewa suna da masaniya ko kuma alaka da harin na karshen mako.

Yankin Niger Delta dai ya yi kaurin suna ta fannin fashi akan teku da kuma satar danyan man fetur, yayin da jami’an tsaro ke iya kokarinsu domin kawo karshen haka.

Barikin sojan Nembe, an kafa shi ne domin fada da masu satar mai a gabar ruwan kasar, kuma wannan ne hari na farko da aka kai wa barikin daga lokacin da aka rantsar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.