MEND ta dauki alhakin kai hari kan 'yan sanda a Bayelsa
Kungiyar fafutukar kare yankin Niger Delta a Najeriya MEND, ta dauki alhakin kai hari kan wasu jiragen ruwan sintirin ‘yan sanda 2 a ranar asabar da ta wuce a jihar Bayelsa.
Wallafawa ranar:
A sanarwar da ta aike wa kafafen yada labarai, kungiyar ta ce ta kai harin ne a yankin Perembari da ke kudancin karamar hukumar mulkin Ijaw saboda jiragen na dauke da wani mai suna Eris Paul daya daga cikin tsoffin jami’anta da a yau ta ke kallo a matsayin maciyi amana.
Har ila yau kungiyar ta ce harin ya yi kama da wanda ta taba kai wa a ranar 6 ga watan Afrilun shekarar 2013 inda ta kashe ‘yan sanda 15 da ke sintiri a yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu