Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kwace wani jirgin ruwa shake da Fetir a Bayelsa

Rundunar Sojin ruwan Najeriya tace ta kwace wani jirgin ruwa shake da lita miliyan biyu da dubu dari na danyan man fetur a Jihar Bayelsa, wanda aka sace. Kwamnadan rundunar sojin, Rear Admiral Sidi Ali Hassan Usman ya tabbatar da haka yana mai cewa sun kama mutane 21 da ake zargi da satar man.

Wasu mazauna kauyen Orobiri, a yankin Niger Delta sun taru a kusa da wani bahon da ke shake da danyen man Fetir
Wasu mazauna kauyen Orobiri, a yankin Niger Delta sun taru a kusa da wani bahon da ke shake da danyen man Fetir REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Satar danyan mai a Najeriya dai ta zama ruwan dare inda tattalin arzikin kasar ya dogara kacokan ga fitar da danyen man.

Rundunar sojin ruwan tace barayin sun gaza gabatar da takardun fitar da danyen mai daga lasisin Kamfanin NNPC kuma babu wani izini da suka samu daga hedikwatar sojin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.