Isa ga babban shafi
Najeriya

Fashewar bututun mai ya hallaka mutane 3 a Najeriya

Mutane 3 sun mutu wasu da dama sun jikkata sakamakon fashewar wani bututun mai a yankin Naija Delta dake Najeriya.

Wani bututun mai da ya fashe a yankin Niger Delta a shekara ta 2009
Wani bututun mai da ya fashe a yankin Niger Delta a shekara ta 2009 AFP
Talla

Rahotanni na cewa bututun man da ya fashe mallakin Kamfanin hakar mai na Eni na kasar Italiya ne, kuma ya fashe ne a daidai lokacin da ake kan yiwa bututun gyara.

Al’amarin ya auku ne a wani yanki mai suna Olugboboro dake jahar Bayelsa tun ranar lahadin da ta gabata sai dai kuma a jiya litinin aka iya gano gawarwakin mutanen ukun

Kawo yanzu dai babu bayani daga Kamfanin ko bangaren gwamnati kasar game da wannan al’amari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.