Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gargadi tsagerun Niger Delta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi tsagerun yankin Niger Delta da yanzu haka ke fasa bututun man fetir da su shiga taitayin su, inda yake cewa murkushe su ba zai zama wahala ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. RFI Hausa
Talla

Yayin da yake jawabi a Hadaddiyar daular larabawa wato Dubai, Buhari ya ce ganin yadda sojojin Najeriya suka murkushe boko haram, samun nasara kan barayin mai da masu satar mutane a yankin ba zai zama wahala ba.

Shugaban ya kuma gargadi kamfanonin sadarwar da ke kasar da su daina fifita riba akan tsaron kasa, inda ya bukaci kamfanonin da ke aiki a Najeriya da su mutunta dokokin kasar.

Buhari ya yi alkawarin cewar duk wanda ya taka doka, doka za ta hau kansa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.