Isa ga babban shafi

Tsoffin Jami’an gwamnati da Gwamnoni sun saci kudaden Najeriya

Gwamnatin Najeriya tace tsoffin jami’an gwamnatin kasar da ‘yan kasuwa da ma’aikatan bankin sun sace kududen talakawa da suka kai Dala biliyan shida da rabi a cikin shekaru bakwai, abin da ya dada jefa kasar ta shiga halin kunci.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Muhammed
Ministan yada labaran Najeriya Lai Muhammed fmi.gov.ng
Talla

Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ne ya bayyana haka, yana mai cewa mutane 55 kacal suka sace wadanann makudan kudade.

Ministan yace wadanda suka sace kudaden sun hada da tsoffin gwamnoni da Ministoci da shugabannin 'Yan kasuwa da wasu jami'an gwamnati da banki tsakanin shekaru 2006 zuwa 2013.

Lai Muhammed ya ce tsoffin Gwamnoni 15 sun saci kudade Naira Biliyan 146. 'Yan kasuwa kuma sun saci kudade da suka kai Naira Biliyan 653.

Sannan ya ce Jami'an Banki sun saci kudade Naira biliyan 524, yayin da  jami'an gwamnati a Jihohi da na Tarayya suka saci kudade Naira Biliyan 14.

Ministan yada labaran yace wannan ne dalilin da ya sa gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsaya kan lalle sai an karbo kudaden na talakawa da aka wawushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.