Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a binciki manyan tsoffin Sojin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci a kaddamar da bincike akan wasu manyan hafsosjin sojin kasar kusan guda 17 da ake zargin suna da hannu dumu dumu ga badakalar wawushe kudaden sayo makaman yaki da kungiyar boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. RFI Hausa
Talla

Sanarwar da ofishin shugaba Buhari ya fitar tace tsohon babban hafsan sojin kasar Alex Badeh na daga cikin mutane 17 da ake zargi wajen wawushe kudaden sayo makamai.

Kuma za a binciki rawar da manyan tsohoffin jami’an sojin suka taka da kuma wasu kamfanoni da dama a badakalar da ta shafi ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Sambo Dasuki na sayo makamai domin yakar Boko Haram.

Sanarwar ta kara da cewa wasu jirage masu saukar Angulu da kayan yaki da aka sayo ba na kirki ba ne a zamanin tsohuwar gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan.

Tuni dai mahukuntan Najeriya ke farautar mutanen da Sambo Dasuki rabawa kudaden sayo makaman bayan hukumar da ke yaki da rashawa a kasar EFCC ta kame shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.