Isa ga babban shafi
Angola

Annobar cutar shawara ta hallaka mutane 51 a Angola

A Kasar Angola mutane 51 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon bullar annobar cutar shawara da aka fi sani da Yellow Fever, akwai kuma wasu akalla 241 dake jinyar cutar a yanzu

Shugaban kasar Angola, Jose Eduardo dos Santos
Shugaban kasar Angola, Jose Eduardo dos Santos AFP PHOTO / STEPHANE DE SAKUTIN
Talla

Wannan dai  shine karon farko a tsawon shekaru 30 da ake sake samun annobar cutar a Angola, cutar da aka ce sauro ke yadawa.

Alamomin cutar sun hada da ciwon kai da amai da kasala kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar.

Yanzu haka dai an yi nasarar yiwa mutane sama da 450,000 riga-kafi yawanci a Luanda babban birnin kasar inda aka fi samun yawan wadanda ke dauke da kwayar cutar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.