Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaban Angola ya kai ziyara Faransa bayan shekaru 20 ya na kauracewa kasar

Bayan shekaru da dama da aka kwashe zaman doya da manja tsakanin Faransa da Angola, shugaba Eduardo Dos Santos na Angola ya kai ziyara a Paris, inda ya gana da takwaransa Francois Hollande, ziyarar da masana siyasar duniya ke ganin za ta iya bude sabon babin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Faransa, Francois Hollande (hagu) da takwaransa Eduardo Dos Santos na Angola (Dama)
Shugaban Faransa, Francois Hollande (hagu) da takwaransa Eduardo Dos Santos na Angola (Dama) REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Rabon dai da Shugaba Santos ya kai ziyara kasar Faransa, tun shekaru kusan ashirin da suka gabata.

Rabon kuma da ya kai ziyara nahiyar Turai, tun a shekarar 2009 inda ya je kasar Portugal.

Shugaban na Angola zai kwashe kwanaki biyu ne a wannan ziyara, a wani yunkuri na sabunta dangantaka dake tsakanin kasashen biyu, tun bayan tankiyar da aka samu a shekarun 1990’s, kan wasu makamai da Faransa ta sayarwa Angola, lamarin da ya shafi huldar kasuwancin manyan kafunan kasar Faransa.

Bayan wata liyafa da ya yi da Hollande a wannan ziyara, Santos ya kuma gana da Ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius da kuma wasu ‘yan kasuwar kasar.

Kasar Faransa, itace kasa ta uku a jerin kasashen da suka fi huldar kasuwanci a Angola, inda take juya kudade da yawansu ya kai kusan miliyan 100 na dalar Amurka.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.