Isa ga babban shafi
Burundi

AU ta jingine matakin tura dakaru Burundi

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta jingine matakin aikawa da dakaru domin aikin wanzar da zaman lafiya a Burundi mai fama da rikici, sakamakon adawa da matakin daga bangaren gwamnatin kasar.

Shugaban Chadi Idriss Deby ya karbi ragamar shugaban Tarayyar Afrika daga Shugaba Mugabe na Zimbabwe
Shugaban Chadi Idriss Deby ya karbi ragamar shugaban Tarayyar Afrika daga Shugaba Mugabe na Zimbabwe REUTERS
Talla

Shugabannin Kungiyar sun amince su tura wakilai a taron da suka gudanar a Addis Ababa domin sasanta rikicin kasar.

Da farko Kungiyar AU ta yanke matakin tura Dakaru kimanin 5000 saboda kazancewar rikici a Burundi inda aka kashe daruruwan mutane a rikicin kasar da aka soma tun a watan Afrilu lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya ayyana kudirin tsayawa takara wa’adi na uku.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Burundi na dab da fadawa yakin basasa kamar irin wanda ya faru a tsakanin 1993 zuwa 2006.

Yanzu haka ‘Yan kasar Burundi dubu dari biyu da talatin ne suka tsere daga kasar zuwa makwabta, sakamakon fargabar tashin hankali.

Gwamnatin Burundi kuma ta ki amincewa da bukatar tura sojojin wanzar da zaman lafiyar na Afrika, saboda ba a tuntubeta ba kafin yanke shawarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.